IQNA

Sayyid Nasrullah Ya Gana Da Ziyad Nakhala Na Kungiyar Jihadul Islami Ta Falastinu

23:05 - March 30, 2022
Lambar Labari: 3487107
Tehran (IQNA) Babban sakataren kungiyar Hizbullah ta kasar Labanon Sayyid Hassan Nasrullah ya gana da babban sakataren kungiyar jihadul Islami ta Falasdinu a safiyar yau.

Tattaunawar ta zo ne domin tattaunawa kan abubuwan da suka shafi yankin da ma kasa da kasa da kuma irin ci gaban da aka samu a yankin Falasdinu da kuma ayyukan jihadi da ake gudanarwa a yankunan falasdinawa da Isra’ila ta mamaye a shekara ta 1948.

Haka zalika ya ce muna mika sakon taya murna ga Alummar falasdinu da irin jarumtar da mujahidansu suka nuna na kai hari tsakiyar abokan gaba a yankuna falasdinawa da suka mamaye .

Har ila yau kungiyar hizbullah ta jaddada cewa hare-haren day an gwagwarmaya suka suka kai da irin mataken da suke dauka wajen fadada ayyukansu ayankin ya nuna cewa zaman da maciya amana suka yin a daidaita hulda da Isra’ila da larabawa ba zai iya lamunce tsaro ga gwammatin Isra’ila ba

Kimanin mutane 5 ne aka kashe yayin da wasu guda 6 kuma suka jikkata a harbe-harbe da aka yi a gabashin birnin Bnai Brak, Zia Hamara sheikh da ya fito daga garin Jenin a Arewa maso yammacin kogin Jodan shi ne ya kai harin neman shahada a yankin.

 

 

 

 

https://iqna.ir/fa/news/4045681

 

captcha