IQNA

Shugabannin Iran Da Iraki Sun Tattauna Kan Muhimmancin Kara Fadada Alaka Tsakanin Kasashensu

18:38 - April 04, 2022
Lambar Labari: 3487123
Tehran (IQNA) shugabannin kasashen Iran da Iraki sun jaddada wajabcin kara fadada alaka a tsakaninsua dukkanin bangarori.

Shugaban kasar Iran Ibrahim Ra’isi a wata zantawa da yayi ta wayar tarho da takwaransa na kasar iraki Barham Salih ya taya shi murnar fara Azumin watan Ramadan mai Alfarma,kuma yayi Alummar Iraki da ma musulmi duniya fatan samun rahamar Ubangiji, kana ya Jaddada cewa Iran tana goyon bayan hadin kai da yancin Alummar Iraki dama tsaron yankin baki daya .

A zantawar tasu shuwagabannin biyu sun nuna cewa kasashen ba wai makwabta ne kawai bay an uwa juna ne kuma suna da daddiyar dangantaka tsakaninsu, kuma an dauki matakai na ganin an bunkasa dangantakar dake tsakaninsu , kuma muna duba yi wuwar sake fadada dangantaka tsakanin a bangarori daban daban da zai taimaka wajen kusantar juna a mataki na kasa da kasa

Haka zalika Ibrahim Ra’isi ya Jadada game da muhimmancin samar da tsaro da zaman lafiya a yankin ba tare da tsoma bakin wasu yan kasashen waje ba, yace lokaci ya tabbatar da jawabin da jagoran juyin musulunci na Iran Ayatollah Ali Khamenei ya yi inda yake cewa Amurka bata tausayin kasashen musulmi a yankin musamman a iraki , kuma ya kara tabbatar da cewa yan kaashen waje suna kare maslaha da manufofinsu na mamaya ne kawai a yankin.

Ana sa bangaren shugaban Kasar Iran Barham Saleh bayan taya muranar shiga watan Ramadan ya jadda game da muhimmancin yin aiki tare tsakanin kasashen biyu domin tun karar kalubalen da yankin yake fuskanta, yace samar da zaman lafiya da tsaro a yankin yana da muhimmanci sosai, kuma muna da kyakkyawar fata game da rawar da Iran za ta taka a wannan bangaren.

 

 

https://iqna.ir/fa/news/4046383

captcha