IQNA

Kungiyar Al-Azhar Watch ta yi gargadi kan cin zarafi ga matan Musulman Indiya

17:35 - April 07, 2022
Lambar Labari: 3487139
Tehran (IQNA) Kungiyar Al-Azhar Watch ta yi gargadi kan ci gaba da cin zarafin mata musulmin Indiya a yanar gizo, inda ta yi kira da a samar da kwararan hanyoyin shari'a da za su hukunta wannan ta'addanci da kuma hukunta masu laifi.

A rahoton da shafin yanar gizo na Al-Wafd ya bayar,

Kungiyar sa ido ta Al-Azhar Watch ta kira irin tsangwamar da ake yi wa musulmi a kasar a hannun ‘yan addinin Hindu masu tsatsauran ra’ayi da cewa, hakan take hakkin bil adama ne, da kuma nuna wariya ta addini , da kokarin danne tsiraru marasa rnjaye a kasar.

Sakamakon wannan mawuyacin hali, musulmi musamman mata daga cikinsu, suna fuskantar matsaloli da dama a kasar.

Bayanin ya ce, akwai takunkumi da dama kan matan musulmin Indiya da sunan yaki da tsatsauran ra'ayi, wanda ya saba wa dokar  'yancin gudanar da addini da kuma zabin tufafin da kowa ya ga dama daidai ra’ayinsa ko akidarsa, kamar yadda kuma da yawa daga cikin wadannan matan na fuskantar cin zarafi, wariya da tsangwama musamman a shafukan Intanet da kafofin sada zumunta, wanda ya zama dandali na yada wadannan muzgunawa.

Kungiyar ta kara da cewa: A cikin shekaru biyar da suka gabata, yawan laifukan da ake aikatawa kan mata musulmi a Indiya ya karu, sannan wasu shafukan yanar gizo da aikace-aikacensu sun yi tasiri wajen kara yawaitar ayyukan cin zarafi da kai wa matan musulmi hari da wulakanta su.

 

https://iqna.ir/fa/news/4047361

captcha