IQNA

Za a gudanar da tattakin ranar Qudus ta duniya a birnin London

23:53 - April 11, 2022
Lambar Labari: 3487155
Tehran (IQNA) Za a gudanar da muzaharar ranar Qudus ta duniya a birnin Landan a ranar Juma'ar karshe ta watan Ramadan tare da halartar kungiyoyin Musulunci da na kare hakkin bil'adama da dama da kuma wasu baki da aka gayyata.

A cewar kungiyar kare hakkin dan Adam ta Musulunci a birnin Landan, Muzaharar wacce hukumar kare hakkin bil'adama ta Musulunci ta shirya, za ta fara ne da karfe 3 na yamma a wajen ma'aikatar harkokin cikin gida ta kuma kare a kan titin Downing. Bakin da aka gayyata za su yi jawabai masu yawa.

A cikin wata sanarwa da kungiyar ta fitar ta ce "Wannan taron wata dama ce ga al'ummar duniya baki daya domin hada kai don yakar tsattsauran ra'ayi na akidar sahyoniyawa .

Gwamnatin wariya ta Isra'ila ta yi imanin cewa za ta iya kawar da Falastinawa sakamakon hare-haren da take kaiwa kan al'ummar falastinu tare da samun taimakon manyan kasashen duniya, musamman kasar Amurka da sauran kasashen turai, wadanda ba su taba daukar mataki kan kisan kiyashin da take yi wa al'ummar Falastinu ba.

Magoya bayan zanga-zangar sun hada da In Minds, Palestine Solidarity Campaign (PSC Scotland), Kwamitin Hulda da Jama'a na Musulman Burtaniya (MPACUK), Kungiyar Hadin Kan Musulunci ta Ahlul Bayt (AIM), kungiyar Yahudawa ta Neturei Karta, Kungiyar Kare Hakkokin Bil'adama ta Musulunci (IHRC). kungiyar yahudawa masu adawa da Isra'ila ta (JNP), kungiyar Scotland Against Criminal Societies, kungiyar dalibai Musulmi a Turai, Football Association Against Apartheid da Ahlul Bayt Society sisters.

Ranar Kudus ta duniya ita ce ranar Juma'ar karshe da marigayi Imam Khumaini wanda ya kafa jamhuriyar Musulunci ta Ira ya ayyana domin nuna goyon baya ga Palastinawa.

A shekarar da ta gabata, sakamakon bullar cutar Corona, musulmi da masu fafutukar kare hakkin Falasdinu a Biritaniya sun gudanar da bukukuwan ranar Kudus ta yanar gizo.

 

 

 

https://iqna.ir/fa/news/4048325

captcha