IQNA

Rahoto: Mutane Fiyec Da Miliyan 17 Na Fuskantar Barzanar Yunwa A Kasar Yemen

19:09 - May 10, 2022
Lambar Labari: 3487275
Tehran (IQNA) Hukumar wanzar da zaman lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana a cikin wani rahoto da ta fitar cewa kimanin ‘yan kasar Yemen miliyan 17 ne ke fama da matsalar karancin abinci, al’amarin da ke kara dagula halin rayuwa a kasar.

Hukumar wanzar zaman lafiya ta duniya ta bayyana hakan ne a cikin wani sabon rahoto da ta fitar, inda ta bayyana cewa a halin yanzu sama da ‘yan kasar Yemen miliyan 17.4 na fama da karancin abinci wanda kuma yunwa za ta iya kassara rayuwarsu.

Sanarwar ta kara da cewa, idan yanayin ya ci gaba haka ba tare da daukar wani matakin gaggawa ba, za a samu karin mutane miliyan 1.6 daga nan zuwa wata mai kamawa da za su kara fadawa cikin irin wannan matsala.

Hukumar ta ce a cikin rahoton nata, tattalin arzikin kasar Yemen ya ragu da kashi 50 cikin 100 tun daga shekara ta 2015 da Saudiyya ta fara kaddamar da hari kan al’ummar kasar, kuma a halin yanzu ana kallon kasar a matsayin daya daga cikin kasashe mafi talauci a duniya, inda kusan kashi 80 cikin 100 na 'yan kasar Yemen ke fama da matsanancin talauci.

Kungiyar ta ce babbar hanyar magance matsalar karancin abinci a kasar Yemen ita ce ci gaba da kara yawan kayan agaji da ake kaiwa a kasar, tare da magance musabbabin wannan matsala tun daga tushenta.

 

4055736

 

 

captcha