IQNA

Jami'in Majalisar Dinkin Duniya:
15:25 - May 19, 2022
Lambar Labari: 3487311
Tehran (IQNA) Wani jami'i a Majalisar Dinkin Duniya, yayin da yake bayyana damuwarsa kan rufe makarantun 'yan mata a Afganistan, ya rubuta cewa: "Ya kamata a dage takunkumin da aka sanya wa 'yan mata a fannin ilimi."

Kamfanin dillancin labaran Anadolu na kasar Turkiyya ya habarta cewa, shugabar ofishin kula da ayyukan jin kai ta MDD, OCHA, Isabel Mossard Carlsen, ta bayyana a shafinta na Twitter cewa, daliban na yau likitoci ne, ma'aikatan jinya, malamai da injiniyoyi na gobe.

Da take bayyana damuwarta game da rufe makarantun 'yan mata a Afganistan, ta rubuta cewa: "Ya kamata a dage takunkumin ilimi a kan 'ya'ya mata. Ilimi wani muhimmin hakki ne na 'yan mata da mata a kowace al'umma."

Idan dai ba a manta ba, bayan da gwamnatin rikon kwarya ta Taliban ta hau kan karagar mulki a kasar Afganistan a shekarar da ta gabata, an hana dalibai mata (makarantar tsakiya da sakandare) shiga azuzuwa.

4058112

 

 

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: