IQNA

17:54 - May 23, 2022
Lambar Labari: 3487330
Tehran (IQNA) Wata kotun Isra'ila a Nazarat ta yanke hukuncin daurin shekaru 5 a gidan yari da kuma tarar kudi a kan fursunoni 5 daga cikin fursunonin da suke gudu daga gidan kaso ta hanyar haka rami a karkashin kasa, wadanda Falastinawa ke kiransu da fursunonin  “Ramin ‘Yanci.”

Hukuncin kotun ya hada da karin shekaru 5 da watanni 8 da tarar shekel 5,000.

A nata bangaren kuma, hukumar kula da harkokin fursunoni ta Falastinu ta bayyana a cikin wata sanarwa bayan yanke hukuncin cewa: Kotunan sojin Isra'ila sun kammala jerin ramuwar gayya kan fursunonin ramin 'yanci da hukuncin rashin adalci.

A nata bangaren, lauya Hanan Khatib daga hukumar kula da harkokin fursunoni ta ce: Ma'aikatar tsaron Isra'ila ba ta son jin wani bayani daga daga fursunonin shida, "kuma wannan bakin ciki ne, amma fursunonin sun tsaya kai da fata wajen yin fatali da hukuncin, tare da shan alwashin kalubalatarsa.

Fursunonin shida sune: Mahmoud Ardah (shekaru 46), daga Arrabeh, gundumar Jenin, Yaqoub Qadri (shekaru 49), daga gundumar Arrabeh Jenin, Ayham Kammji (shekaru 35), daga Kfardan, Munadil Infa'at (shekaru 26), daga Ya'bad, gundumar Jenin, Muhammad Ardah (shekaru 40), daga Arrabeh, gundumar Jenin, da Zakaria Zubeidi (shekaru 45), daga Jenin.

4058916

 

 

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: Yanke Hukunci ، Fursunoni ، gidan yari ، tarar kudi ، karkashin kasa
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: