IQNA

Wani Matashi Bafalastine Ya Yi Shahada A Yau Sakamakon Harbinsa Da Da Sojojin Isra'ila Suka Yi

15:48 - June 25, 2022
Lambar Labari: 3487463
Tehran (IQNA) Majiyoyin gwamnatin Falasdinawa sun sanar a yau Asabar cewa, sojojin Isra’ila sun harbe wani matashi bafalstine har lahira a yau garin Salwad da ke Ramallah.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Amad cewa, Abdullah Muhammad Hamad ya samu raunuka masu muni  sakamakon harbin bindigar da sojojin yahudawan Isra’ila suka yi masa a yau, wanda daga bisani kuma ya yi shahada.

Dakarun gwamnatin yahudawan sahyuniya sun tsananta kai hare-haren wuce gona da iri kan matasan Palasdinawa a cikin 'yan watannin nan, inda suka kashe Palasdinawa 70 tun farkon wannan shekara ya zuwa yanzu.

Kafofin yada labaran Falasdinu sun kuma bayar da rahoton cewa, an jikkata mutane 131 a arangamar da suka yi da 'yan ta'addar yahudawan a yayin tattakin da Falasdinawa suka yi a yammacin ranar jiya Juma'a, inda suka yi Allah wadai da gine-ginen matsugunan da aka yi a wurare daban-daban na Falastinawa da Isra’ila ta mamaye.

Dukkanin abin da ya ke faruwa kan al’ummar Falastinu an cin zalun da kisan kiyashi da Isra’ila ke yi, yana faruwa ne a kan idanun duniya, , ba tare da wata kasa daga cikin amnyan kasashen da ke da’awar kare hakkin bil adama sun ce uffan ba.

4066364

 

Abubuwan Da Ya Shafa: wani matashi ، bafalastine ، shahada ، kisan kiyashi ، gine-gine
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
captcha