Kimanin alhazai miliyan guda ne suka fita domin tsayuwar ta arfa inda za su kwashe yinin ranar wato tun daga zawali zuwa faduwar rana suna addu’oi kafin daga bisani su wuce zuwa Muzdalifa.
Ranar Arfa ita ce rana mafi girma da muhimmnanci a duka kwanakin aikin hajji.
A wannan shekarar 2022, arfa ta fado a ranar Jumma’a, kuma ba kasafai ake samun ranar ta fado a Jumma’ar ba.
Haka kuma za a yi hawan arfa na shekarar dubu biyu da ashirin da biyu ne bayan shafe shekara biyu alhazai daga wasu kasashe ba su halarci aikin hajji ba saboda bullar annobar korona.
Hakan ne y asa hukumomin Saudiyya suka kayyade adadin mahajjatan shekarar zuwa miliyan guda.