IQNA

An kashe wani jigo a kungiyar Taliban a wani harin ta'addanci da ISIS ta kai

15:45 - August 12, 2022
Lambar Labari: 3487676
Tehran (IQNA) Majiyoyin labarai sun sanar da cewa an kashe wani jigo a kungiyar Taliban sakamakon fashewar wani bam a wata makarantar addini a Kabul.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Tolo News cewa, wani babban jigo na kungiyar Taliban ya mutu sakamakon fashewar wani abu a wata makarantar addini da ke gundumar ta biyu a birnin Kabul.

A cewar majiyoyin, wannan fashewar ta faru ne da yammacin yau Alhamis 11 ga watan Agusta a makarantar addini ta Rahimullah Haqqani da ke yankin Shashdarak a birnin Kabul.

Rahotanni sun bayyana cewa, a cikin wannan fashewar wasu 'yan ta'addar Taliban guda goma ne suka mutu, ciki har da Rahimullah Haqqani, daya daga cikin manyan jami'an Taliban kuma shugaban wannan makaranta.

Kungiyar ta'addanci ta Da'esh ta dauki alhakin harin da aka kai a wata makarantar addini a Kabul, babban birnin kasar Afganistan, inda aka kashe wani jigo na kungiyar Taliban.

Tashar talabijin ta TART ta bayar da rahoton cewa, kungiyar ISIS ta dauki alhakin kai harin, wanda ya girgiza babban birnin kasar ta Afganistan sa'o'i kadan da suka gabata.

 

 

4077470

 

Abubuwan Da Ya Shafa: Taliban ، birnin kabul ، makaranta ، babban jigo ، addini
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
captcha