IQNA

An Ba da lambar yabo ta harkokin kudi na musulunci ta Duniya ga Firayi Ministan Habasha

16:40 - September 16, 2022
Lambar Labari: 3487864
Tehran (IQNA) An bayar da lambar yabo ta kudi ta Musulunci ta Duniya ga Abiy Ahmed, Firayim Minista na Habasha.

Kamar yadda Iqna ta ruwaito; Kamfanin dillancin labaran Anatolia ya habarta cewa, firaministan kasar Habasha Abiy Ahmed ya samu lambar yabo ta fuskar kudi ta Musulunci a taron kolin kudi na kasashen musulmi na duniya saboda kokarin da ya yi na farfado da fannin hada-hadar kudi na kasarsa.

Ahmed ya bayyana jin dadinsa da samun wannan lambar yabo a lokacin da yake jawabi a wajen bikin karramawar.

An gudanar da taron koli na harkokin kudi na kasashen musulmi a kasar Djibouti.

An tuna cewa Abiy Ahmed Kirista ne na Pentecostal kuma ɗan siyasa daga Habasha kuma Firayim Minista na 12 na Habasha. Shi ne shugaban jam'iyyun adawa na Habasha da na Oromo People's Democratic Organization, da kuma mamba a majalisar wakilan kasar Habasha kuma mamba a kwamitin gudanarwa na OPDO da EPRDF. Ya lashe kyautar zaman lafiya ta Nobel a shekarar 2019.

4085896

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: Firayi Minista ، Habasha ، bikin karramawa ، lambar yabo ، musulunci
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
captcha