IQNA

Wakiliyar Majalisar Dinkin Duniya ta saka hijabi a hubbaren Imam Hussain (AS)

17:07 - December 12, 2022
Lambar Labari: 3488324
Tehran (IQNA) Wakiliyar musamman ta babban sakataren MDD a kasar Iraki Jenin Henis Plaskhart wadda ta je Karbala ta ziyarci haramin Imam Husaini (AS) inda ta gana da Sheikh Abdul Mahdi Karbalai mai kula da haramin Hosseini.

Kamfanin dillancin labaran kur’ani na iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na kasar Iraki cewa, Wakiliyar musamman ta babban sakataren MDD a kasar Irakin da ta je birnin Karbala a jiya ta bayyana a hubbaren Imam Husaini (AS) sanye da hijabi inda ta ziyarci sassa daban-daban na hubbaren.

Yayin da take ishara da ganawar da Paparoma ya yi da Ayatollah Sistani da kuma ganawar da ya yi da mahukuntan kasar Irakin, ya ce wannan taron ya hada Alkahira, Najaf Ashraf da fadar Vatican, wadanda ake daukar su a matsayin ginshikan addinai guda uku a kewayen  duniya.

A cikin wadannan, za ku ga bidiyo biyu na wakilan Majalisar Dinkin Duniya a Haramin Imam Hosseini.

Kuna iya ganin bidiyon kyauta ta musamman da hubbaren Imam Hosseini ya yi wa wakiliyar Majalisar Dinkin Duniya a Iraki.

 

 
 
 

 

captcha