
Kamfanin dillancin labaran kur’ani na iqna ya habarta cewa, cibiyar sadarwar “Al-Shorouk” ta kasar Aljeriya tana shirya gasa ta kasa da kasa domin haddar kur’ani mai tsarki da ake yi wa lakabi da zabura na Dauda a kasashen Larabawa da na Musulunci a kowace shekara.
Matakin farko na wannan gasa ana gudanar da shi ne ta hanyar WhatsApp, kuma mahalartan da suka yi nasarar samun nasara za su shiga matakin karshe na wannan gasa.
An gudanar da wannan zagayen gasa tare da halartar mahalarta daga kasashe 10, kuma Sheikh Issa Al-Masrawi, fitaccen makarancin Masar, shi ne shugaban kwamitin alkalai.
Yara ‘yan shekara 10 zuwa 16 da suka haddace kur’ani ne suka halarci wannan gasa da tashar tauraron dan adam ta Al-Sharooq ta kasar Aljeriya ta shirya tare da watsa shirye-shiryenta.
An gudanar da wadannan gasa ne a kasar Aljeriya a watan da ya gabata kuma Ahmad Azfar Azraei, wani hazikin yaro dan kasar Malaysia mai shekaru 10, ya samu nasarar lashe matsayi na daya a wadannan gasa tare da bajinta mai ban mamaki.
A wani bangare na wannan taron na kur'ani, Ahmad Azfar ya karanta suratul Mubaraka Balad tare da mahaifinsa, wanda shahararren makaranci ne dan kasar Malaysia.