Kamfanin dillancin labaran IQNA ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Ghana Soccer Net cewa, a wannan aikin agajin da aka gudanar a watan azumin Ramadan, Ayew ya bayar da gudummawar buhun shinkafa da galan na man girki ga kowanne daga cikin wadannan mabukata. Abokin Ayew Abdul Razzaq wanda aka fi sani da DJ Carlos ne ya raba wadannan gudummawar a Jubilee Park a garin Tamale jiya.
Wannan dai ba shi ne karon farko da Ayew ke nuna jajircewarsa na taimakon mabukata a yankinsa ba. A lokacin cutar ta Covid-19, ya samar da magungunan kashe kwayoyin cuta da abin rufe fuska ga mutanen Ghana don taimaka musu su kare kansu daga cutar.
A cikin 2019, Ayew kuma ya ba da gudummawar kuɗi ga ƙungiyar Ghana U20.
Ayew, wanda musulmi ne kuma mai shekaru 33 a duniya, a halin yanzu yana cikin kungiyar Nottingham Forest a gasar firimiya ta kasar Ingila, kuma ya buga wasanni 113 na kasa da kasa da kuma kwallaye 24 a kungiyar ta Ghana.