IQNA

Tunawa da Sayyed Makavi, ma’abucin karatun Asmaullah al-Husna

14:25 - April 25, 2023
Lambar Labari: 3489035
Tehran (IQNA) Sayyid Mohammad Seyyed Makkawi shahararren makaranci ne dan kasar Masar, wanda har yanzu ana amfani da fitattun ayyukansa da suka hada da Asmaullah al-Husna a lokacin buda baki a tsawon shekaru masu yawa.

Kamfanin dillancin labaran kur’ani na iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Misri Alyoum cewa, a garinsu na kasar Masar, mutane da dama sun san shi da kyakkyawar muryarsa a farkon watan Ramadan.

Yawancin mutanen Masar da suka yi kuruciyarsu a shekarun 1970 suna tunawa da kyakkyawar muryar "Mashrati" sanye da wata doguwar farar riga da abaya mai kyakykyawan ado mai ruwan zinare rike da karamar ganga yana kada ta, kuma wata karmar  yarinya ce ta rike hannunsa tana kai shi kan tituna da unguwannin Alkahira a lokacin sahur yana tayar da mutane.

Masharati yana rera waka:

Tashi, daga barci, da...

Wadannan hotuna da kasidu da wakoki su ne abubuwan tunawa da dimbin al'ummar Masarawa suke tunawa da shi, da haka Sayyed Makavi ya zama a raye a cikin zukatan  mutanen Masar.

A kasar Iran akwai mutane da suke kwaikwayon irin wannan aiki nasa wanda sun shahara a cikin watan Ramadan ana sanya karatunsu an Asmaullah al-Husna a lokacin buda baki.

Ya rasu a ranar 21 ga Afrilu, 1997 yana da shekaru 70. Duk da haka, abin day a gadar na fasaha da na addini yana nan a raye, daga ciki har da dawwamammen aiki na " Asmaullah al-Husna".

4136273

 

captcha