A cikin watan Muharram kuma a ranakun zaman juyayin shahidar Aba Abdullah Al-Hussein (AS), IQNA ta fitar da karatun suratu Fajr da sautin fitattun mahardata na duniya. A kashi na uku kuma za a ji karatun suratul Fajr cikin muryar Abdul Basit Muhammad Abdul Samad, shahararren makaranci a duniyar Musulunci.