IQNA

Rundunar 'yan sandan Melbourne za ta kare tarukan ranar Ashura

18:40 - July 27, 2023
Lambar Labari: 3489546
Melbourne (IQNA) Rundunar 'yan sandan birnin "Melbourne" ta kasar Ostireliya ta sanar da cewa za ta samar da tsaro ga tarukan ranar Ashura a wannan birni da za a yi a ranar Asabar.

'Yan sandan jihar Victoria sun ce suna sa ran tsakanin mutane 3,000 zuwa 5,000 za su halarci taron na ranar Asabar, kamar yadda jaridar Star ta ruwaito.

'Yan sandan Victoria sun ce suna tsammanin taron zai kasance cikin kwanciyar hankali.

"Za mu kasance a yankin don tabbatar da tsaron lafiyar mahalarta," in ji sanarwar 'yan sanda. Muna sa ran ganin wannan muhimmin taro ya zamanto mai aminci ga masu taron. 'Yan sandan Victoria suna mutunta haƙƙin ɗaiɗaikun mutane don aiwatar da tarukansu.

Akwai Musulmi mabiya mazhabar Shi'a kusan 30,000 a kasar Australiya.

 

4158488

 

 

captcha