IQNA

Isra’ila na barazanar kaddamar da hare-hare a kan Asibitin Qudus A Gaza

19:23 - October 21, 2023
Lambar Labari: 3490014
Gaza (IQNA) Asibitin Qudus na Gaza yana da majinyata sama da 400 kuma yana dauke da mutane 12,000 da suka rasa matsugunansu, galibinsu mata da kananan yara. Har ila yau, a daren jiya (28 ga watan Oktoba) da aka kai hare-haren bama-bamai a wasu gine-ginen da ke kusa da asibitin, mutane da wadanda suka jikkata sun fake a asibitin Shafa da ke zirin Gaza.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na al-Qastal cewa, likitocin asibitin na Quds ba su bar wuraren aikinsu ba duk da barazanar da Isra’ila ke yi musu.

Ma'aikatan jinya na asibitin al-Quds da ke Gaza sun sanar da cewa ba za su bar wannan wuri ba saboda barazanar da sojojin yahudawan sahyoniya suke yi na kai harin bam a asibitin.

A wata hira da Al Jazeera, babban darektan ma'aikatar kiwon lafiya ta Gaza ya bayyana cewa: Dole ne mu ci gaba da aikinmu har zuwa lokacin karshe. Ba za mu taɓa barin wannan wurin ba.

Asibitoci a zirin Gaza a halin yanzu suna cike da 'yan gudun hijirar Falasdinu.

Za ku iya kallon asibitin al-Quds a Gaza, wanda ke cike da mata da yara da suka rasa matsugunansu.

 

 

4176728

https://iqna.ir/fa/news/4176728

Abubuwan Da Ya Shafa: asibiti quds barazanar hare-hare kiwon lafiya
captcha