IQNA

Haramta kayayyakin yahudawan sahyoniyawa a Indonesia

16:34 - November 14, 2023
Lambar Labari: 3490150
Jakarta (IQNA) Al'ummar Indonesiya sun goyi bayan fatawar majalisar malamai ta wannan kasa tare da kauracewa kayayyakin gwamnatin sahyoniyawan.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a cewar tashar talabijin ta Aljazeera, al'ummar Indonesia sun fara kauracewa kamfanin McDonald's da sauran kayayyakin gwamnatin ne a tsakiyar watan Oktoba bayan da reshen McDonald na Isra'ila ya goyi bayan sojojin mamaya na Haramtacciyar Kasar Isra'ila a shafin Instagram tare da sanar da cewa za su samar da abinci kyauta ga sojojin wannan gwamnatin ta yahudawa.

Sanarwar ta sa kungiyoyi da dama na Indonesiya, da suka hada da Boycott and Sactions Movement (BDS), People's United Front (FUB), da Islamic Defenders Front (FPI), suka yi kira da a kaurace wa kamfanin McDonald's da sauran harkokin kasuwanci masu goyon bayan sahyoniya, ciki har da Starbucks. da Burger King..

Haramcin ya zo ne a daidai lokacin da kamfanin McDonald na Indonesiya mallakin kamfanin samar da abinci na kasa PT Rekso, ya sanar a makon da ya gabata cewa ya bayar da gudunmuwar rupiah biliyan 1.5 na Indonesiya kwatankwacin dalar Amurka 96,000 a matsayin agajin jin kai don tallafawa Falasdinawa.

Ad Andrian, daya daga cikin darektocin wata kungiyar agaji a Indonesia, ya kasance yana siyayya a McDonald's tare da iyalinsa akalla sau daya a wata.

Andrian ya gaya wa Al Jazeera: Odar da na fi so ita ce abincin iyali; Ko kuma idan zan tuƙi, koyaushe ina yin odar ice cream.

Amma tun a watan da ya gabata, a matsayin martani ga kiraye-kirayen da aka yi a duk kasar Indonesia na kauracewa kamfanin McDonald da sauran kayayyakin gwamnatin sahyoniyawan, ya hana saye daga wannan gidan abincin. Ya ce: "Tun da muka gano cewa McDonald's na Isra'ila yana taimakawa sojojin wannan gwamnatin, ban sake zuwa McDonald's ba."

Indonesiya, kasa mafi yawan al'ummar musulmi a duniya, ta dade tana tausayawa al'ummar Palastinu, kuma gwamnatin sahyoniya ba ta da ofishin jakadanci a kasar.

A makon da ya gabata ne Majalisar Malamai ta Indonesiya (MUI) wacce ita ce babbar cibiyar Musulunci a kasar Indonesia ta fitar da wata fatawa da ke bayyana goyon bayan zaluncin gwamnatin sahyoniyawan a kan Falasdinu ko kuma yin mu’amala da bangarorin da ke goyon bayan gwamnatin sahyoniyawan kai tsaye ko a kaikaice, a matsayin haramun.

 

4181712

 

 

captcha