IQNA

Shahid Hazem Haniyyah yana karatun kur'ani mai girma

16:11 - April 14, 2024
Lambar Labari: 3490984
IQNA - Bidiyon karatun kur’ani da shahid Hazem Haniyeh ya yi a daya daga cikin masallatan Gaza ya samu karbuwa daga wajen masu amfani da shafukan sada zumunta.

Kamfanin dillancin labaran kur’ani na iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Yeni Shafaq cewa, hoton shahid Hazem Haniyeh yana karanta ayoyin suratu Mubaraka Ibrahim (a.s) a daya daga cikin masallatan Gaza, ya samu karbuwa daga masu amfani da shafukan sada zumunta.

A cikin wannan faifan bidiyo shahid Hazem Haniyeh dan Ismail Haniyeh shugaban ofishin siyasa na kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Falasdinawa (Hamas) yana karanta wadannan ayoyi na suratu Mubaraka Ibrahim cikin murya da murya mai dadi.

Shahid Hazem Haniyeh tare da ‘yan uwansa biyu Amir da Mohammad da kuma wasu ‘yan uwa da dama sun yi shahada a ranar Larabar da ta gabata, daidai da Sallar Idi, a wani hari da mayakan yahudawan sahyoniyawan suka kai kan motar da ke dauke da su.

 

 

 4210091

 

Abubuwan Da Ya Shafa: dauke da mayakan yahudawa hamas karatu kur’ani
captcha