IQNA

Jagoran Ansarullah A Yamen:

Amurka Na Hankoron Shimfita Ikonta Ne A Kan Kasashen Musulmi

14:48 - June 26, 2024
Lambar Labari: 3491408
IQNA - Jagoran kungiyar Ansarullah ta kasar Yemen a wani jawabi da ya gabatar a yayin zagayowar ranar Idin Ghadir ya sanar da cewa, Amurka a matsayinta na mai girman kai a wannan zamani tana kokarin dora mulkinta kan musulmi.

Tashar Almasirah ta bayar da rahoton cewa, Shugaban kungiyar Ansar Allah ta Yaman, Sayyed Abdul-Malik al-Houthi, ya ce Amurka na neman dora ikonta a kan musulmi, inda ta dora kanta a matsayin kwamandan rundunar da ke tsara manufofi.

A yayin da yake gabatar da jawabi kan bikin al-Ghadir, Sayyed al-Houthi ya yi nuni da cewa, Amurka na tsoma baki cikin harkokin kasashen musulmi a dukkan bangarori, da kuma kokarin dora ikonta kan al'ummar musulmi.

Shugaban na Ansarllah ta Yemen ya bayyana Amurka a matsayin "kasa mafi girman kai ta wannan zamani" ya kuma zargi Washington da neman dora abin da ya kira "hukuncin zalunci " a kan musulmi da kuma sarrafa su a cikin dukkanin al'amuransu yadda tag a dama.

Ya koka kan yadda gwamnatoci  da dama ke bin Amurka ido rufe, ya kara da cewa wasu daga cikin bangarorin suna kokarin yakar wadanda suka ki amincewa da wannan zalunci an Amurka.

A cewar Sayyed al-Houthi, wasu gwamnatocin kasashen musulmi, da shugabanni, da sarakuna, sun amince da ikon Amurka a kansu, sun kuma mika mata wuya tana jan akalarsu zuwa inda tag a dama.

Ya kara da cewa wadanda suka yarda da wannan suna bin umarnin Washington, suna gujewa abin da ya saba ma siyasarta,  da kuma adawa da duk wanda baya biyayya gare ta ko ya saba mata.

 

4223150

 

captcha