Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Al-Alam cewa, hare-haren da sojojin yahudawan sahyuniya suka kai cikin dare a yankunan tsakiya da kudancin zirin Gaza sun yi sanadin mutuwar mutane akalla 9 tare da jikkata wasu da dama.
Sojojin Isra'ila sun ci gaba da kai hare-hare a yankuna daban-daban na zirin Gaza a rana ta 286 a jere tare da haddasa babban bala'i.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na ‘Wafa’ cewa, jiragen yakin haramtacciyar kasar Isra’ila sun yi ruwan bama-bamai a wani gida a yankin Al-Zawaida da ke sansanin ‘yan gudun hijira na Nusirat da ke tsakiyar yankin zirin Gaza, inda suka kashe Falasdinawa 6 tare da jikkata wasu da dama.
A cikin shirin za a ji cewa, harin da mayakan gwamnatin sahyoniyawan suka kai kan masallacin Abdallah Azam da ke sansanin 'yan gudun hijira na Nusirat ya yi sanadin mutuwar akalla mutum guda tare da jikkata wasu 15 na daban.
Mutane 2 ne suka yi shahada, mutane 7 suka jikkata, kana wasu yara 4 suka bace a harin sama da sojojin yahudawan sahyoniya suka kai a wani gida da ke sansanin 'yan gudun hijira na El Brij da ke tsakiyar yankin zirin Gaza.