Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na sakatariyar kungiyar majalisun dokokin kasashen kungiyar hadin kan kasashen musulmi, wannan sakatariyar ta nuna damuwa tare da yin Allah wadai da wannan mataki, inda ta fitar da sanarwa game da rufe cibiyoyin muslunci a birnin Hamburg da sauran garuruwan Jamus.
Sanarwar ta ce: Wadannan cibiyoyi suna ba da hidimar al'adu da na ruhi ga musulmi tsiraru a Jamus, kuma rufe su ya sabawa ka'idojin 'yancin dan adam musamman 'yancin addini da imani. Kungiyar Hadin Kan Musulunci tana ganin wadannan matakan da suka yi hannun riga da ka'idojin kare hakkin bil'adama tare da jaddada wajabcin kiyaye 'yancin walwala.
Sanarwar ta kuma yi gargadin cewa irin wadannan ayyuka na iya haifar da karuwar tashe-tashen hankula, da haifar da kiyayya, kyamar Musulunci da cin zarafi ga musulmi da kuma yin mummunan tasiri kan zaman lafiya a tsakanin mabiya addinai daban-daban. Kungiyar Majalisun Dokokin Kungiyar Hadin Kan Musulunci da ke goyon bayan hakkokin Musulmi tsiraru a duniya, ta yi kira ga mahukuntan Jamus da su yi nazari tare da yin watsi da wadannan hukunce-hukuncen da ke cutar da musulmi.