kafofin yada labaran Najeriya sun bayar da rahotanni da cewa, Magoya bayan Harka Islamiyya a Najeriya sun gudanar da jerin gwano a birane daban-daban na kasar domin nuna rashin amincewa da kuma yin tir da Allawadai da cire wa mata musulmi hijabi da 'yan sanda suka yi a ranar da suka gudanar da tattakin arbaeen a birnin Abuja.
Majiyoyin Harka Islamiyya sun bayyana cewa, magoya bayan Harkar sun gudanar da jerin gwano na tattakin arbaeen a birnin Abuja, yayin da jami'an tsaro na 'yan sanda suka auka musu da duka da harba barkonon tsohuwa a kansa.
A nasu bangaren jami'an 'yan sanda sun zargi magoya bayan Harka da kai musu hari da jifar jami'ansu da duwatsu, da kona musu motoci gami da kashe 'yan sanda biyu a yayin tattakin.
To sai dai majiyoyin Harka Islamiyya sun karyata wannan zargi, tare da bayyana cewa jami'an 'yan sandan suka fara auka musu a lokacin da suke jerin gwano na lumana, kuma basu da hannu a kona motocin 'yansanda da kuma kisan jami'an 'yan samda biyu da ake zarginsu da aikatawa.