A bisa rahoton Newarab, Macron wanda ya ziyarci wannan kasa biyo bayan gayyatar da sarki Mohammed na shida ya yi masa, ya fuskanci zanga-zanga daga jama’a masu adawa da manufofin faransa na goyon bayan Isra’ila.
Kungiyar 'Morocco for Palestine', wata kungiya ce ta cikin gida mai adawa da daidaita alaka da gwamnatin sahyoniyawan ta ce: Ba mu yin maraba da Macron a kasarmu saboda goyon bayansa ga gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila da kuma manufofinsa na zalunci ga 'yan gwagwarmayar Palastinu.
Kungiyar "Tallafawa Falasdinu" da ke Rabat ita ma wata kungiyar da ke adawa da manufofin Faransa, wadda ita ma ta gudanar da zanga-zanga a gaban majalisar dokoki a daidai lokacin da Macron ya isa a wurin.
Shugaban kasar Faransa ya gabatar da jawabi a majalisar dokokin kasar Maroko a ranar 29 ga watan Oktoba a ziyarar ta kwanaki uku da ya kai kasar ta Morocco, wadda ita ce ta farko da ya kai a kasar, tun daga shekarar 2018, wadda ta kunshi tattaunawa kai-tsaye tsakanin shugabannin kasashen biyu, tare da rattaba hannu kan yarjejeniyoyin makamashi da ruwa da ilimi da kuma tsaro.
Da farko Faransa ta haramta zanga-zangar goyon bayan Falasdinu a farkon yakin da Isra'ila ke yi a Gaza, duk da cewa kotun kolin kasar ta yi gaggawar soke hukuncin.
A baya Macron ya ce kyamar sahyoniya tana daidai da kyamar Yahudawa kuma ya kamata a dauki hakan a matsayin laifin kiyayya.