Masu zanga-zangar sun yi Allah wadai da hare-haren da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila ke kai wa zirin Gaza da Lebanon.
Sun yi ta rera taken nuna goyon baya ga Falasdinu tare da jaddada cewa nasara ta gwagwarmaya ce.
Har ila yau, suna dauke da tutoci masu rubuta, "Gaza za ta yi nasara", da "Dukkanmu Gaza ne, Mu duka Falasdinu ne".
An gudanar da muzaharar ne bayan sallar Juma'a a mako na 57 a jere don amsa kiran wata kungiya mai zaman kanta mai suna "Tallafawa Al'amuran Al'ummah".
Fez, Casablanca, Tetouan, Meknes, Guercif, Agadir da Berkane na daga cikin biranen da suka gudanar da zanga-zangar, a cewar kamfanin dillancin labarai na Anadolu.
A watan Oktoban shekarar da ta gabata ne gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila ta kaddamar da yakinta na kisan kare dangi a zirin Gaza, inda ya zuwa yanzu ta kashe Falasdinawa sama da 146,000 da kuma jikkata wasu.
Har ila yau, tana kai hare-hare kan kasar Lebanon, inda ta tsananta kai hare-hare a cikin 'yan watannin da suka gabata.