IQNA

Rarraba kwafin kur'ani 10,000 a wajen bikin a lardin Al-Hariq na kasar Saudiyya

14:32 - January 12, 2025
Lambar Labari: 3492552
IQNA - Ma'aikatar kula da harkokin addinin musulunci ta Saudiyya ta sanar da raba sama da kwafin kur'ani mai tsarki 10,000 a yayin bikin citrus karo na tara a lardin Al-Hariq.

A cewar Shahad Naw, ofishin kula da harkokin addinin muslunci na kasar Saudiyya da ke birnin Riyadh, ya raba fiye da kwafin kur’ani mai tsarki guda dubu 10 masu girma da bugu daban-daban, wanda cibiyar buga kur’ani ta Sarki Fahd da ke Madina ta buga a tsakanin maziyartan rumfar. Ma'aikatar ta raba a bikin Citrus karo na 9 a lardin Al-Hariq, wanda aka kaddamar a farkon watan Rajab 1446 bayan hijira.

An gudanar da bikin ne tare da halartar manyan jami’an gwamnati da na jama’a da gungun manoma da suka baje kolin kayayyakinsu a wajen bikin, kuma ya kare a ranar Juma’ar da ta gabata.

Cibiyar harakokin muslunci ta baje kolin kur'ani mai tsarki da tarjamarsa zuwa harsuna daban daban na duniya. Sama da kwafin kur’ani mai tsarki 10,000 da ruwayoyi daban-daban da kuma littafin Tafsirin Maysir ne aka ware domin rabawa maziyartan baje kolin a yayin bikin, ta yadda maziyartan za su samu kwafin wannan littafi.

Maziyartan Bikin Citrus sun yaba da kokarin ma'aikatar kula da harkokin addinin musulunci, da'awah da jagoranci wajen yi wa addinin musulunci da musulmi hidima, da kuma ci gaba da kasancewa a lokuta daban-daban na kasa da na addini, da na'urorin lantarki a fagen wa'azi da shiryarwa ta hukumar. 

Idan dai ba a manta ba, lardin Al-Hariq na daya daga cikin lardunan yankin Riyadh na kasar Saudiyya, mai tazarar kilomita 200 daga Riyadh, babban birnin kasar Saudiyya. Wannan lardi yana a Wadi Na'am a yankin Jabal Tuwaiq a kudancin Najd, kuma mazauna yankin sun fito ne daga kabilar Al-Hazazana.

 

 

4259448

 

 

captcha