Al-Kafeel ya nakalto Sayyed Muhannad Al-Miyali, darektan cibiyar kur’ani mai tsarki ta Najaf mai alaka da majalissar kur’ani mai tsarki ta haramin Abbasid yana cewa: “Wannan gasar kur’ani ta kasa da kasa tana musamman ne ga daliban makarantar hauza na Najaf, kuma ana gudanar da ita da manufarta na qarfafa ilimin Alqur'ani da fahimtar Alqur'ani."
Ya kara da cewa: A farkon tantancewar da aka yi a gasar, an zabo dalibai dari, inda aka zabo mahalarta 40 daga kasashen Musulunci 10.
Al-Miyali ya bayyana cewa: Mahalarta gasar sun fafata a fannoni daban-daban da suka hada da haddar sassa 5 da haddar sassa 10 da haddar Alkur'ani gaba daya da kuma bangaren tadabburi da bincike a cikin kur'ani.
Ya kara da cewa: Wannan gasa wata dama ce ga daliban makarantar Najaf wajen kara ilimin kur'ani ta hanyar fahimta da tawassuli da tafsirin kur'ani tare da karfafa karatun kur'ani da tajwidi.