Ministan harkokin cikin gida na Jamhuriyar Nijar Mohamed Toumba ya sanar da cewa mutane da dama ne suka yi shahada ko kuma suka jikkata sakamakon harin ta'addanci da aka kai kan masu ibada a kasar.
A cewar Anadolu, lamarin ya faru ne a kauyen Fonbita da ke yankin Kokorou.
Harin dai ya faru ne a jiya da yamma a lokacin da masu ibada ke gudanar da sallar Juma'a a lokacin da 'yan ta'adda dauke da makamai suka kewaye su tare da yi musu kisan gilla.
Akalla mutane 44 ne suka mutu inda wasu 13 suka jikkata a wannan harin na ta'addanci.
Gwamnatin Nijar ta ayyana zaman makoki na kwanaki uku a fadin kasar daga ranar Asabar zuwa Litinin na wannan mako.
Kamar yadda hukumomin tsaron Nijar suka ruwaito, 'yan ta'addar ISIS a Afirka (ISGS) ne suka kai wannan harin na zubar da jini.
A cewar wani rahoto da kafar yada labarai ta Sahara Media dake wallafa labaran Afirka, an kashe akalla fararen hula 44 a jiya Juma'a, a wani hari da makami da aka kai a wani kauye da ke kudu maso yammacin jamhuriyar Nijar kusa da iyakar kasashen uku na Nijar da Burkina Faso da kuma Mali.