IQNA

Zaman Lafiya Ya Kasance Mafi Kyau: Shugaban Al Azhar Ya Yaba Da Tsagaita Wuta tsakanin Indiya da Pakistan

1:07 - May 13, 2025
Lambar Labari: 3493250
IQNA – Babban Limamin Al-Azhar na kasar Masar ya yaba da yarjejeniyar tsagaita bude wuta da aka sanar a tsakanin Indiya da Pakistan bayan da ya nuna damuwa game da takun saka tsakanin kasashen biyu masu makamin nukiliya a cikin ‘yan kwanakin nan.

Sheikh Ahmed al-Tayeb ya rubuta a shafinsa na Facebook a ranar Lahadi cewa "Muna maraba da yarjejeniyar tsagaita bude wuta tsakanin Indiya da Pakistan a matsayin wani muhimmin mataki na bunkasa zaman lafiya, tsaro, da kwanciyar hankali a Kudancin Asiya da ma duniya baki daya."

"Zaman lafiya ya kasance mafi kyawun zabi wanda ya kamata ya jagoranci dangantaka tsakanin kasashe da al'ummomi. Saboda haka, dole ne a karfafa kokarin kasa da kasa don kawo karshen duk rikice-rikice, yaƙe-yaƙe, da kuma tashin hankali, ta yadda bil'adama za su ji dadin duniya mafi kyau da ke cike da aminci, alheri, da wadata," in ji al-Tayeb.

A ranar Asabar ma gwamnatin Masar ta yi marhabin da sanarwar tsagaita wuta tsakanin Indiya da Pakistan.

Makwabtan kudancin Asiya masu dauke da makaman kare dangi sun amince da tsagaita bude wuta a ranar asabar bayan shafe kwanaki hudu ana gwabza fada - mafi muni a cikin shekaru da dama -wanda ke yin barazanar rikidewa zuwa yakin basasa.

Sakataren harkokin wajen Indiya ya sanar da cewa, kasashen biyu sun amince su dakatar da fadan nan take, wanda zai fara aiki da karfe 5 na yamma (1130 GMT) a ranar Lahadi, bayan tattaunawa tsakanin shugabannin sojojinsu.

Ministan Harkokin Wajen Pakistan Ishaq Dar ya tabbatar a kan X: "Pakistan da Indiya sun amince da tsagaita wuta cikin gaggawa."

An bayar da rahoton mutuwar fararen hula da dama tare da jikkata wasu da dama a musayar hare-haren da Indiya ta kaddamar a matsayin mayar da martani ga kisan gillar da aka yi wa mutane 26 mafi yawansu 'yan yawon bude ido Indiya a watan da ya gabata a yankin Kashmir da ke karkashin ikon Indiya.

 

3493059

 

 

captcha