Abin da ke tafe shi ne cikakken sakon Ayatullah Sayyid Ali Khamenei:
Da sunan Allah, Mai rahama, Mai jin kai
Zuwa ga al'ummar Iran mai girma!
Da gari ya waye a yau gwamnatin Sahayoniya ta aikata wani laifi a kan kasarmu abin kauna, inda ta bayyana mugunyar aniyarta ta zubar da jini. Ta hanyar kai hari ga wuraren zama na jama'a, ta sake bayyana mugun halinta fiye da kowane lokaci. Dole ne a yanzu wannan gwamnati ta jira hukunci mai tsanani.
Da izinin Allah, hannu mai karfi na dakarun Jamhuriyar Musulunci ba zai bari wannan ta'addanci ya tafi ba tare da mayar da martani ba. A cikin hare-haren abokan gaba, wasu daga cikin kwamandojinmu da masana kimiyya sun yi shahada. Wadanda suka gaje su da abokan aikinsu in Allah ya yarda za su ci gaba da gudanar da ayyukansu nan take.
Da wannan laifin, gwamnatin Sahayoniya ta shirya wa kanta makoma mai ɗaci da raɗaɗi, kuma babu shakka za ta fuskanci hakan
Sayyid Ali Khamenei
4288154