Abbas al-Bahadli kakakin ma'aikatar harkokin cikin gidan kasar Irakin ya bayyana cewa, kasar ta karbi bakuncin maziyarta miliyan 4 da dubu 100 daga tawagogin kasashen waje da suke halarci tarukan Arbaeen.
Ya kara da cewa wannan adadin masu ziyara daga kasashe 140 ne suka halarci Arbaeen na wannan shekara.
Tun da farko dai shugaban sashen yada labarai na tsaro na Iraki ya jaddada cewa, kawo yanzu babu wata matsala ta tsaro a wannan tattaki.
Shi ma gwamnan Karbala, al-Mu’alla, ya ce adadin maziyarta ya karu idan aka kwatanta da bara.
A yayin zagayowar ranar Arbaeen, shugaban kasar Iraki Badal al-Latif al-Rashid ya jajantawa masu ziyara da jami'an tsaro, da tawagogin makokin Imam Hussaini.
Ya ce: A ranar Arba'in na Imam Husaini (AS) yana mika ta'aziyya ga al'ummar Iraki, da al'ummar musulmi, da kuma hukumar kula da harkokin addini, tare da tunawa da gagarumar jarumtaka da sadaukarwa da Jagoran shahidai Imam Husaini (AS) ya jagoranta wajen fuskantar zalunci da yaki da fasadi.