Shafin yada labarai na Al-Furat ya bayar da rahoton cewa, a yau alhamis ne Haramin Imam Husaini (AS) ya sanar da fara kai agajin gaggawa ga al’ummar Gaza, a wani bangare na gangamin “Hajjin Arba’in” tare da goyon bayan Ayatullah Sayyid Ali Sistani, babban mai kula da harkokin addini. Manufar bayar da wannan tallafin ita ce rage radadin da al'ummar Gaza ke ciki.
Muhammad Yousef mamba na tawagar Haramin Imam Husaini (AS) da ke zirin Gaza yana mai cewa: "Don dakile manufofin yunwa da yahudawan sahyoniyawan suke yi, a yau a matsayin wani bangare na gangamin tattakin Arba'in da kuma goyon bayan Ayatullah Sayyid Ali Sistani, muna raba abinci ga al'ummar yankin arewacin Zirin Gaza da aka yi wa kawanya."
Yousef ya ci gaba da cewa: Ana gudanar da aikin raba kayan ne tare da gudunmawar da aka bayar na Haramin Imam Husaini (AS).