IQNA - An gudanar da sallar mamaci ne a kan gawar shahid Mujahid Ismail Haniyeh shugaban ofishin siyasa na kungiyar Hamas a birnin Doha, tare da halartar dubun dubatan masu ibada.
Lambar Labari: 3491622 Ranar Watsawa : 2024/08/02
IQNA - Babban Mufti na masarautar Oman ya yi Allah wadai da kisan gillar da gwamnatin sahyoniya ta yi wa Ismail Haniyya shugaban ofishin siyasa na kungiyar gwagwarmaya ta Hamas a birnin Tehran, yana mai jaddada cewa gwagwarmayar Palastinawa za ta ci gaba da kasancewa a cikinta da kuma tafarkin shahidan Haniyyah. za a ci gaba.
Lambar Labari: 3491619 Ranar Watsawa : 2024/08/01
IQNA - A safiyar yau ne aka gudanar da jana'izar shahid Ismail Haniyeh shugaban ofishin siyasa na kungiyar Hamas tare da halartar jama’a da dama, da kuma jawabin Mohammad Baqer Qalibaf shugaban majalisar dokoki Iran .
Lambar Labari: 3491618 Ranar Watsawa : 2024/08/01
Sakon ta'aziyyar jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran bayan shahadar Ismail Haniyya:
IQNA - A cikin sakonsa na cewa, Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya yi ta'aziyyar shahadar babban mujahidin Isma'il Haniyyah shugaban ofishin siyasa na kungiyar Hamas inda ya ce: Hukumar 'yan ta'adda ta Sahayoniyya ta shirya tsatsauran hukunci ita kanta da wannan aiki, da ta aikata a cikin yankin Jamhuriyar Musulunci Iran , kuma martini kan hakan wajibi ne a kanmu.
Lambar Labari: 3491611 Ranar Watsawa : 2024/07/31
IQNA - Shugaban ofishin huldar kasa da kasa na kungiyar Hamas ya dauki bayanin na birnin Beijing a matsayin wani mataki mai kyau a kan hanyar samun hadin kan al'ummar Palasdinu, haka kuma kungiyar Jihadin Islama ta sanar da cewa, ba za ta taba yin nauyi da duk wata dabara da ta amince da gwamnatin sahyoniyawan ba.
Lambar Labari: 3491578 Ranar Watsawa : 2024/07/25
IQNA - Akalla mutane 40 ne suka yi shahada yayin da wasu da dama kuma suka jikkata sakamakon harin da Isra’ila ta kai kan tantunan ‘yan gudun hijira a wani sansani da ke arewa maso yammacin garin Rafah a kudancin Zirin Gaza.
Lambar Labari: 3491230 Ranar Watsawa : 2024/05/27
IQNA - Yakin da ake yi a yankin zirin Gaza na baya-bayan nan ya jawo hankulan jama’a da dama ga kungiyar Hamas daga ayoyin kur’ani mai tsarki da sunayen shahidan Palastinawa na bayyana sunayen makaman da ake amfani da su a wannan jihadi.
Lambar Labari: 3490391 Ranar Watsawa : 2023/12/30
Kungiyar Hamas ta yi Allah wadai da sabon takunkumin da Amurka da Birtaniya suka kakaba wa masu gwagwarmayar Palasdinawa ta hanyar fitar da sanarwa.
Lambar Labari: 3490315 Ranar Watsawa : 2023/12/15
Gaza (IQNA) A daidai lokacin da aka kawo karshen yarjejeniyar tsagaita bude wuta na jin kai a zirin Gaza, sojojin gwamnatin sahyoniyawan mamaya sun sake kai hare-hare a wannan yanki ta sama da kasa a safiyar yau. Sakamakon wadannan hare-haren Palasdinawa da dama sun yi shahada tare da jikkata.
Lambar Labari: 3490235 Ranar Watsawa : 2023/12/01
Hamshakin attajirin nan dan kasar Amurka Elon Musk ya yi watsi da gayyatar da kungiyar Hamas ta yi masa na ziyartar zirin Gaza a wani sakon da ya wallafa a shafin sada zumunta na "X" a safiyar Larabar da ta gabata ya kuma rubuta cewa: Ziyarar Gaza na da matukar hadari a halin yanzu.
Lambar Labari: 3490225 Ranar Watsawa : 2023/11/29
Washingto (IQNA) Majalisar Wakilan Amurka ta amince da daftarin kudirin yin Allawadai da ‘yar majalisar wakilai ‘yar asalin Falastinu Rashidah Tlaib, daga Michigan, bisa goyon bayan al’ummar Palasdinu.
Lambar Labari: 3490115 Ranar Watsawa : 2023/11/08
Tehran (IQNA) Wakilin kungiyar Hamas a Iran ya bayyana cewa: Guguwar Al-Aqsa za ta kai ga mabubbugar nasara da alkawarin Allah da taimakonsa, kuma musulmin duniya za su yi salla tare a masallacin Aqsa.
Lambar Labari: 3490090 Ranar Watsawa : 2023/11/04
Gaza (IQNA) Kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Palasdinawa ta Hamas ta yi kira ga al'ummar Larabawa da na Musulunci da kuma al'ummar duniya masu 'yanci da su fara gudanar da gangami a wannan Juma'a domin sake bude kan iyakar Rafah da kuma dakatar da yakin kisan kare dangi a zirin Gaza.
Lambar Labari: 3490045 Ranar Watsawa : 2023/10/27
Halin da ake ciki a Falasdinu
Bayan kazamin harin kasa da makami mai linzami da mayakan Palasdinawa suka kai kan yankunan da aka mamaye, kwamitin sulhu na MDD na gudanar da wani taron gaggawa a yau. A gefe guda kuma dakarun gwagwarmayar na Lebanon sun kai hari kan sansanonin sojojin yahudawan sahyoniya da dama.
Lambar Labari: 3489941 Ranar Watsawa : 2023/10/08
Tehran (IQNA) Kasar Saudiyya ta saki dan babban dan kungiyar Hamas kuma tsohon wakilin wannan yunkuri a Saudiyya daga gidan yari.
Lambar Labari: 3489049 Ranar Watsawa : 2023/04/27
Tehran (IQNA) Kungiyar Hamas ta yi kira ga daukacin Falasdinawa a Yammacin Gabar Kogin Jordan da Kudus da kuma yankunan da aka mamaye da su kalubalanci yunkurin gwamnatin sahyoniyawan na Yahudawa wuri mai tsarki tare da dimbin kasancewarsa a Masallacin Al-Aqsa.
Lambar Labari: 3487458 Ranar Watsawa : 2022/06/23
Tehran (IQNA) kungiyar kasashen larabawa ta fitar da bayanin yin maraba da matakin da kungiyar tarayyar Afirka ta dauka na jingine batun baiwa Isra'ila kujerar a matsayin mamba mai sanya idoa kungiyar.
Lambar Labari: 3486920 Ranar Watsawa : 2022/02/07
Kungiyar gwagwarmayar Falastinawa ta Hamas ta yi Allah wadai da ziyarar da firayi ministan Isra'ila ya kai kasar Hadaddiyar daular larabawa.
Lambar Labari: 3486684 Ranar Watsawa : 2021/12/14
Tehran (IQNA) Hamas ta yi maraba da kalaman ministan harkokin wajen kasar Aljeriya kan kin amincewa da daidaita alaka da Isra'ila.
Lambar Labari: 3486551 Ranar Watsawa : 2021/11/13
Tehran (IQNA) Masar ta sanar da rufe mashigar Rafah wadda ta hada iyakokin kasar da yankin zirin Gaza na Falastinu.
Lambar Labari: 3486232 Ranar Watsawa : 2021/08/23