New Jersey (IQNA) A ranar Asabar 31 ga watan Yulin wannan shekara ne al'ummar Shi'a na garin Carteret da ke jihar New Jersey ta kasar Amurka za su gudanar da muzahara domin karrama Imam Hussain (AS).
Lambar Labari: 3489511 Ranar Watsawa : 2023/07/21
Jagoran juyin juya halin Musuluncin ya bayyana a cikin sakonsa ga mahajjatan bana:
Tehran (IQNA) Ayatullah Khamenei a cikin wani sako da ya aike kan babban taron Hajjin bana, ya bayyana aikin Hajji a matsayin kira na daukakar dan Adam a duniya, kuma wani tushe ne na daukakar ruhi da dabi'u na bil'adama, ya kuma jaddada cewa: sharadin da ya wajaba wajen ingancin aikin Hajji a duniya shi ne. Madaidaicin fahimtar al'ummar musulmi da kuma fahimtar wannan magana ta rayuwa ta wannan aiki, asirai sun ginu ne a kan ginshikan "haɗin kai" da "karfafa ruhi".
Lambar Labari: 3489379 Ranar Watsawa : 2023/06/27
An gudanar da zagayen farko na tattaunawar addini tsakanin 'yan uwa musulmi mata da mabiya darikar Katolika da nufin karfafa dangantaka da tattaunawa tsakanin musulmi da kiristoci na kasar Kenya a cibiyar Retreat Subiako dake birnin Karen.
Lambar Labari: 3489308 Ranar Watsawa : 2023/06/14
A taron zaman lafiya da aka yi, an jaddada cewa;
An gudanar da taron kasa da kasa karo na biyu kan zaman lafiya mai taken "Haduwar duniyar Musulunci da wayewar da za ta dore kan manufofin shari'a a nan gaba" a jami'ar Tehran, inda aka jaddada cewa hadin kan tattalin arzikin kasashen musulmi na daya daga cikin manyan abubuwan da suka sa a gaba. wajen fuskantar girman kan duniya.
Lambar Labari: 3489283 Ranar Watsawa : 2023/06/10
Tehran (IQNA) Za a gudanar da taron "Imam Khomeini (RA): Rayayyun Gado" a kasar Kenya ta hanyar shawarwarin al'adu na kasarmu tare da halartar masu tunani daga gabashin Afirka.
Lambar Labari: 3489246 Ranar Watsawa : 2023/06/03
Me Kur'ani ke cewa (50)
Bambancin ra'ayi da ra'ayi wani lokaci yana haifar da rabuwa da nisa tsakanin muminai. Amma Alkur'ani yana kiran kowa zuwa ga hadin kai ta hanyar gabatar da mafita ta musamman.
Lambar Labari: 3489115 Ranar Watsawa : 2023/05/09
Tehran (IQNA) Ana iya kallon komawar kasar Siriya cikin kungiyar hadin kan Larabawa bayan shekaru 12 a matsayin nasara ta hakika na tsayin daka kan makarkashiyar sauya al'amura a yankin domin goyon bayan gwamnatin sahyoniyawan da kuma kasashen yammacin turai.
Lambar Labari: 3489107 Ranar Watsawa : 2023/05/08
A taron malaman kasar Lebanon an jaddada cewa;
Tehran (IQNA) Taron malaman musulmi a kasar Lebanon, ta hanyar shirya wani taro na yin Allah wadai da kona kur'ani da kuma hare-haren ta'addanci da aka kai a kasashen musulmi na baya-bayan nan, sun jaddada cewa hanyar da za a bi wajen kawar da fitina ita ce kiran malaman al'ummar musulmi zuwa ga hadin kai .
Lambar Labari: 3488596 Ranar Watsawa : 2023/02/02
A zantawarsa da Iqna, malamin jami'ar Malaysia ya jaddada cewa;
Tehran (IQNA) Muhammad Fawzi bin Zakariy wani mai tunani dan kasar Malesiya ya ce: hadin kai tsakanin al'ummomin musulmi zai kuma sa gwamnatocin kasashen larabawa su gane cewa sahyoniyanci ba abokiyarsu ba ce, amma zai ci gaba da kasancewa makiyin gamayya na dukkanin musulmi har zuwa lokacin da ake 'yantar da Kudus.
Lambar Labari: 3488020 Ranar Watsawa : 2022/10/16
Mataimakin shugaban majalisar malaman kasar Sham:
Tehran (IQNA) Mataimakin shugaban majalisar malaman kasar Sham ya bayyana cewa: Taron hadin kan kasa da kasa wata dama ce ta zinari ga haduwar musulmi, tare da yin tunani tare a kan matsalolin da kasashen musulmi suke fuskanta, da warware matsalolin da suke fuskanta a fagen rarrabuwar kawuna da cudanya tsakanin musulmi.
Lambar Labari: 3488001 Ranar Watsawa : 2022/10/13
Tehran (IQNA) “Youanes Adib” limamin cocin Katolika na birnin Ghordaqah da ke lardin Bahr al-Ahmar na kasar Masar, ya raba kayan zaki ga al’ummar musulmi a maulidin manzon Allah (SAW).
Lambar Labari: 3487987 Ranar Watsawa : 2022/10/10
Babban sakataren kungiyar kusanto da mazhabobin musulunci:
Tehran (IQNA) Hojjat-ul-Islam wa al-Muslimin Shahriari ya sanar da daidaita alaka da gwamnatin sahyoniyawan da ke mamaya da kuma yin Allah wadai da shi a matsayin babban taken taron hadin kan kasashen musulmi na kasa da kasa karo na 36.
Lambar Labari: 3487979 Ranar Watsawa : 2022/10/09
Tehran (IQNA) Sheikh Khalid al-Molla shugaban kungiyar malaman Sunna na kasar Iraqi ya bada labarin cewa ya tsallake rijiya da baya a wani yunkurin kashe shi a birnin Basra.
Lambar Labari: 3487963 Ranar Watsawa : 2022/10/06
Tehran (IQNA) Jagoran juyin juya halin muslunci na Iran ya bayyana tarukan arbaeen a matsayin wata alama ta hadin kai .
Lambar Labari: 3487804 Ranar Watsawa : 2022/09/05
Tehran (IQNA) an yi kira a kasar Masar ad akawo karshen tozarta cibiyar musulunci ta Azhar da wasu ke yi a kasar.
Lambar Labari: 3487542 Ranar Watsawa : 2022/07/13
Tehran (IQNA) Babban kwamandan dakarun sa kai na al’ummar Iraki Hashd Al-shaabi (Popular Mobilization ) Faleh al-Fayyad, ya yi bayani kan mataki na gaba a kasar Iraki, a daidai lokacin da ake gudanar da bukukuwan cika shekaru 8 da bayar da fatawar kafa dakarun.
Lambar Labari: 3487416 Ranar Watsawa : 2022/06/13
Tehran (IQNA) babban shehin cibiyar Azhar ya yi suka kan yadda ake yin amfani da kalmar addinan Annabi Ibrahim.
Lambar Labari: 3486532 Ranar Watsawa : 2021/11/09
Tehran (IQNA) Ayatollah Muhammad Ali Taskhiri ya bayar da gudunmawa domin ganin an samu hadin kai tsakanin al'ummar musulmi.
Lambar Labari: 3486444 Ranar Watsawa : 2021/10/19
Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci A Iran:
Tehran (IQNA) Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya bayyana cewar Iran ba ta damu kan waye zai lashe zaben shugabancin Amurka ba
Lambar Labari: 3485331 Ranar Watsawa : 2020/11/03
Tehran (IQNA) fiye da masallata dubu 20 ne suka gudanar da sallar juma’a a yau a masallacin Aqsa.
Lambar Labari: 3485301 Ranar Watsawa : 2020/10/23