Kamfanin dilalncin labaran Iqna ya habarta cewa, ya naklto daga shafin sadarwa na yanar gizo na tashar talabijin din Almanar na kasar Lebanon cewa, a wani jawabi da ya gabatar a jiya domin tunawa da ranar shuda, jagoran kungiyar gwagwarmayar muslunci ta Hizbullah a kasar Lebanon Sayyid Hassan Nasrullah ya yi gargadin cewa hadarin da ke tattare da masu akidar kafirta Musulunmi hadari ne da zai shafi dukkanin musulmi da ma wadanda ba musulmi,a cikin kasar Lebanon da ma wajenta.
Babban sakataren kungiyar ta Hizbullah ya ce yana kira ga dukkanin muslulmi da kirista da su kwana da sanin cewa ‘yan takafiriyya mutane ne da bas u dauke da wata akida ta wani addini, mutane da suke hankula daidai da irin ayyukansu na dabbanci, kuma domin kuwa ba su da daga kafa ga kowa, sabani na mahanga zai sanya su kafirta mutum kuma su yanke masa hukunci kisa su kashe shi a nan take.
Sayyid Nasrullah ya bayar da misali kan yadda ‘yan takfiriyya suke kashe junansu a Syria, wadanda suke da mahanga da akida da tunani iri daya, kuma mutum daya ne suke kallo a matsayin shugabansu, amma sabani kan yadda za mallaki ganima ko kuma yadda za a rike wani yanki da suka kame sais u kafirta junasu su kashe kawunansu.
1375962