Kamfanin dillancin labaran Iqna ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gzo na Alwihdainfo cewa, daruruwan mabiya addinin muslunci sun kafa wata runduna domin kare kansu daga farmakin da mabiya addinin kirista suke kai wa a kansu tare da yi musu kisan kiyashi babu gaira babu sabar.
A wani bayanin kuma babban sakatare janar na majalisar dinkin duniya ya gabatar da shawarar aikewa da dakarun kiyaye sulhu na majalisar dinkin duniya zuwa jamhuriyar Afirka ta tsakiya, dmin dawo da doka da oda a kasar.
A cikin wani rahoto da ya aike wa kwamitin tsaron majalisar dinkin duniya dangane da halin da ake ciki a jamhuriyar Afirka ta tsakiya, ya gabatar da shawara ga mambobin kwamitin da ke neman su amince da a aike da dakarun kasa da kasa karkashin inuwar majalisar dinkin duniya zuwa jamhuriyar Afirka ta tsakiya, ya ce aikinsu na farko shi ne kare fararen hula da ke fuskantar kisan gilla a kasar.
Mambobin kwamitin tsaron majalisar dinkin duniya za su yi nazarin wannan shawara, kafin daga bisani su gudanar da zama na musamman kan lamarin, domin yanke matsaya guda kan yadda za a yi aiki da wannan shawara.