Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa, a yayin ganawar da ya yi da sakataren majalisar koli ta tsaron kasar Iran Ali Shamkani a yau a birnin Beirut, Sayyid Hassan Nasarllah ya yi ishara da hadin da ake ciki a yanzu a kasa na barazanar ta’addanci wanda ba shi da tamka a cikin wannan yanki, muhimmin abinda kungiyar Hizbullah ta sanya a gaba shi ne fuskantar wannan ta’addancin na masu akidar kafirta mutane da kuma aiko domin hana shi isowa cikin Lebanon.
Sayyid Hassan Nasarllah ya kuma yi ishara da kokarin da kungiyar ta Hizbullah ta ke yi na ganin an sami zamon lafiya da hadin kan al’ummar kasar. Sayydi Hassan Nasarallah ya kuma jaddada godiya ga Jamhuriyar Musulunci ta iran akan matsayarta na taimakawa gwagwarmaya, tare da cewa; Fuskantar ayyukan ta’addanci na masu akidar kafirta mutane tana da bukatuwa da daukar matakai masu karfi ba wasan kwakwayo ba. A nashi gefen, Sakataren Majalisar tsaron kasar ta Iran Ali Shamkhani ya yabawa kungiyar HIzbullah akan rawar da ta ke takawa wajen kare kasar Lebanon.