IQNA

An Hana Saka Hijabin Musulunci A wasu Makarantun Nigeria

23:12 - October 19, 2014
Lambar Labari: 1461866
Bangaren kasa da kasa, an hana saka hijabi a wasu makarantu a birnin Lagos babbar cibiyar kasuwanci da harkokin tatatlin arzikin kasar wqabnda hakan ya shafi makarantun firamare da kuma bangare na farko na makarantun sakandare.


Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na This Day Live cewa, babbar kotun kolin Najeriya a Jahar Lagos ta fitar da hukuncin hana saka hijabi a wasu makarantu a birnin na Lagos babbar cibiyar kasuwanci da harkokin tatatlin arzikin kasar wabnda ya shafi makarantun firamare da kuma bangare na farko na makarantun sakandare da ke fadin jahar.

Bayanin ya ci gaba da cewa bayan fitar da wanann hukunci wasu daga cikin al’ummomin jahar sun nuna rashin amincewarsu da hakan, tare da yin kira ga kotun da kuma mahukunta na jahar da su yi dubi a kan wannan lamari, domin kuwa zai cutar da dimbin mutane na jahar wadanda akasarinsu mabiya addinin musulunci ne na kabilar yarabawa.

Yanzu haka dai mahukuntan jahar suna ci gaba da karbar irin wadannan korafe-korafe daga dubban mutane na jahar wadanda suke kallon haka a matsayin wani hukunci wanda ya sabawa ‘yancin yin addini tare da bin koyarwa a kasar, wanda kuma kundin tsarin mulkin Najeriya ya bayar da dama ga kowane dan kasa da ya bi duk irin addinin da ya natsu da shi, tare da yin hakan cikin ‘yanci ba tare da wata takurawa ba.

1460995

Abubuwan Da Ya Shafa: lagos
captcha