IQNA

Sayyid Nasrullah Ya Jaddada Wajabcin Fito Da Musulunci Na Hakika A Taron Ashura

20:15 - October 22, 2014
Lambar Labari: 1463056
Bangaren kasa da kasa, babban sakataren kungiyar gwgwarmayar muslunci ta Hizbullah a kasar Lebanon Sayyid Hassan nasrullah ya jaddada wajabcin yin amfani da wannan munasaba domin bayyana wa al'ummomin duniya hakikanin muslunci domin fuskantar ta'addancin Daesh.

Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo an Almanar cewa, a jiya ne babban sakataren kungiyar gwgwarmayar muslunci ta Hizbullah a kasar Lebanon Sayyid Hassan nasrullah ya jaddada wajabcin yin amfani da wannan munasaba domin bayyana wa al'ummomin duniya hakikanin muslunci domin fuskantar ta'addancin Daesh da aka fi sani da ISIS.
Babban sakataren kungiyar Hizbullahi ta kasar Labanon ya bayyana cewar masu dauke da akidar kafirta musulmi suna kokarin bata sunan addinin Musulunci ne tare da raba kan al'ummar musulmin duniya.
A ganawarsa da wakilin shugaban kasar Iran kan harkokin Majalisa a yau Lahadi a birnin Beiruit na kasar Labanon; Babban sakataren kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hizbullahi Sayyid Hasan Nasrullahi ya bayyana cewar masu dauke da akidar kafirta musulmi suna bata sunan Musulunci ne tare da kokarin ganin sun raba kan al'ummar musulmi musamman kunna wutan rikicin mazhaba, don haka Sayyid Hasan Nasrullahi ya gargadi al'ummar musulmi da masu 'yanci na duniya da su kasance cikin fadaka kan wannan mummunar tunani da ke ci gaba da wanzuwa.
A nashi bangaren wakilin jagoran ya yi Allah wadai kan harin wuce gona da irin da jirgin saman sojin haramtacciyar kasar Isra'ila ya kai kan kasar Siriya da kuma ayyukan ta'addanci da 'yan tawayen Siriya ke ci gaba da aiwatarwa a kasar ta Siriya.
1462403

Abubuwan Da Ya Shafa: Nasrullah
captcha