Kamfanin dilalncin labaran Iqna ya nakalto daga shafin sadarw3a na yanar gizo na Almanar cewa a jawabin da ya gabatar na ranar farko na watan Muharram jagoran kungiyar Hizbullah a kasar Lebanon Sayyid Hassan Nasrullah a babban dakin taruka na mabiya mazhabar ahlul bait a birnin berut fadar mulkin kasar ya bayyana barazanar ‘yan ta’adda ba za ta raba mu da Imam Hussain (AS) ba duk kuwa da irin kumajin da suke yi kan hakan.
Sakatare janar na kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hizbullahi Sayyid Hasan Nasrullahi ya bayyana cewar masu dauke da akidar kafirta musulmi suna bata sunan Musulunci ne tare da kokarin ganin sun raba kan al'ummar musulmi musamman kunna wutan rikicin mazhaba, don haka Sayyid Hasan Nasrullahi ya gargadi al'ummar musulmi da masu 'yanci na duniya da su kasance cikin fadaka kan wannan mummunar tunani da ke ci gaba da wanzuwa atsakanin musulmi.
Ya kara da cewa dole ne dukkanin musulmi su zama cikin fadaka domin yin fito-nafito da wannan mummunan tunani da kuma mummunar akida, wadda ke nufin rusa addinin muslunci da koyarwar irin ta addini mai tsarki, wanda kuma hakan shi ne hadari mai girma acikin yaduwar wannan bakar akida.
Sayyid narullah y ace wajibi ne da ya rataya kan dukkanin muslu a dukkanin bangarori na sadarwa da kuma rubutu da siyasa da kuma a hukumance a fuskanci wannan lamari da gaske.
1463795