IQNA

An Nuna Wani Kur'ani Da Aka Danganta Da Imam Sajjad AS A Karbala

17:55 - May 04, 2009
Lambar Labari: 1773959
Bangaren kasa da kasa: An nuna wani kur'ani da aka rubuta da hannu wanda aka danganta da Imam Zainul abiding AS, gami da wasu littafai da tarihinsu ke komawa zuwa shekaru masu yawa a baya.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga shafin internet na kamfanin dillancin labaran kasar Iraki cewa; An nuna wani kur'ani da aka rubuta da hannu wanda aka danganta da Imam Zainul abiding AS, gami da wasu littafai da tarihinsu ke komawa zuwa shekaru masu yawa a baya. Byanin ya ci gaba da cewa wannan baje koli ya samu halartar malamai da masana daga sassa daban-daban na kasar Iraki, musamman ma malaman jami'a daga cikinsu da suke gudanar da nazari kan harkokin tarihin Musulunci. Wani daya daga cikin jami'an da suke jagorantar gudanar da taron baje kolin kayyakin tarihin ya bayyana cewa daya daga cikin manufofin gudanar da wannan baje koli ita ce kara wayar da kan al'ummar Iraki kan tarihin Musulunci da kuma dangantakar da kasar take da ita da hakan.

398561













captcha