Bangaren kasa da kasa; Za a gudanar da gasar karatu da hardar kur'ani mai tsarki a birnin Jidda na kasar saudiyya wadda za a fara gudanarwa a ranar alhamis mai zuwa, kuma wannan shi ne karo na goma sha hudu da ake gudanar da ita.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na arab news an habarta cewa, Za a gudanar da gasar karatu da hardar kur'ani mai tsarki a birnin Jidda na kasar saudiyya wadda za a fara gudanarwa a ranar alhamis mai zuwa, kuma wannan shi ne karo na goma sha hudu da ake gudanar da ita a matsayi na shekara-shekara abirnin na Jiddah.
Bayanin ay ci gaba da cewa wannan gasar karatu da hardar kur'ani kamar yadda aka saba gudanar da ita ta kebanci kanan yara da matasa'yan kasa da shekaru 12, kuma ana fara gudanar da ita ne daga safe zuwa yamma.
Wannan gasa ta hada da yara na 'yan kasashen waje da ke zaune a kasar ta Saudiyya, musamman ma 'yan kasar Philipines, inda karamin ofishin jakadancin kasar da ke Jidda ya ke bayar da tasa gudunwar a gasar.
631003