Bangaren kasa da kasa; An gudanar da zaman taron cika shekara guda da rasuwar shugaban majalisar koli ta Musulunci a kasar Iraki Sayyid Abdulaziz Hakim, tare da halartar wakilan manyan malama addini na birnin.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, kamfanin dillancin labaran kasar Iraki na brana ya habarta cewa, an gudanar da zaman taron cika shekara guda da rasuwar shugaban majalisar koli ta Musulunci a kasar Iraki Sayyid Abdulaziz Hakim, tare da halartar wakilan manyan malama addini na birnin na Najaf mai alfarma.
Taron ya yi dubi ne dangane da irin rawar da Sayyid Abdulaziz Hakim ya taka a bangarori da dama, da hakan ya hada da bangaren rayuwa ta ilimi da kuma rayuwarsa da ya fi yin fice da ita kafin rasuwarsa a bangaren siyasa.
Wadanda suka gabatar da jawabai a wajen taron sun mayar da hankali ne kan irin darussan da za a iya dauka daga rayuwarsa ta sadaukantarwa, da kuma yadda ya kasance mai riko da addini a cikin dukkanin harkoki na siyasa.
635767