Bangaren kasa da kasa; Za a fara gudanar da wani taro na bayar da horo kan ilmomin kur'ani mai tsarki, wanda cibiyar kula da harkokin al'adu da ilimi ta kasashen musulmi ISESCO ta dauki nauyin shiryawa da gudanarwa a kasar Sudan.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani bayani da ya nakalto daga shafin sadarwa na kungiyar ISESCO an bayyana cewa, za a fara gudanar da wani taro na bayar da horo kan ilmomin kur'ani mai tsarki, wanda cibiyar kula da harkokin al'adu da ilimi ta kasashen musulmi ISESCO ta dauki nauyin shiryawa da gudanarwa a kasar Sudan a cikin wannan mako.
Bayanin ya ci gaba da cewa babbar manufar gudanar da wannan taron bayar da horo ita ce kara fitar da koyarwa irin ta addinin muslunci daidai da koyarwar kur'ani, da kuma karfafa musulmi kan yin aiki da abin da ke cikin littafinsu.
Wannan zaman taro zai yi dubi kan muhimmancin shigar da darussan Musulunci a cikin tsari koyarwa na kashen musulmi domin kara sanar da dalibai hakikanin koyarwar addinin Musulunci.
656811