Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na jaridar Al-akhbar cewa, a yayin ganawarsa jagoran kungiyar Hizbullah a kasar Lebanon Sayyid Hassan Nasrullah da tsohon firayi ministan kasar Iraki Nuri Maliki Nasrullah ya jinjina masa kan irin matakan da ya dauka na kin amincewa da Amurka a lokacin mulkinsa.
Kafin wannan ganawar dai Nuri malki ya gana da wasu daga cikin manyan jami'an gwamnatin kasar ta Lebanon da suka hada hard a firayi minista Tamam salam, wanda kuma kafin nan ya gana da wasu fitattun 'yan siyasa, inda ya jaddada wajabcin yin tsayuwar daka wajen fuskantar barazanar ta'addanci a duniya musulmi da larabawa.
Jagoran kungiyar ta hizbullah ya jaddada cikaken goyon bayansa ga irin wadannan matakai da Maliki ya dauka, inda ya sheda cewa dole ne dukkanin al'ummomi su mike domin fuskantar wannan babbar barazana da balai da ya bulla da ke kokari shafa bakin fyanti ga addinin muslunci.
A nasa bangaren Nuri Maliki ya bayyana abin day a faru tsakaninsa da Haidar Ubadi da cewa rashin fahimta ne, amma dai ya zuwa an warware dukkanin matsalolin da aka fuskanta alokacin, kuma suna ci gaba da yin aiki tare.