Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarat cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na tashar talabijin ta Al-mayadeen cewa, a sanarwar da kungiyar Hizbullahi ta fitar a jiya Lahadi ta bayyana cewar Sayyid Hasan Nasrullahi babban sakataren kungiyar ya gana da wakilin shugaban kasar Rasha Mikha’il Bogdanov da mataimakin ministan harkokin wajen kasar ta Rasha da suka ziyarce shi a birnin Beirut na Lebanon a ranar Asabar da ta gabata, inda zaman tattaunawansu ya fi mai da hankali kan batun dambaruwar siyasar yankin gabas ta tsakiya musamman rikicin kasar Siriya da kuma matsalar kasar Lebanon.
Jakadar kasar Rasha a Lebanon Alexander Zasypkin shi ne ya jagoranci tawagar manyan jami’an na kasarsa a ganawarsu da Nasrullahi, sai dai har yanzu babu cikakken labarin matsayar da bangarorin biyu suka cimma a zaman tattaunawan.
Wannan dais hi ne karo na biyu da mataimakin ministan na kasar Rasha yake ganawa da bababn sakataren kungiyar ta gwagwarmaya.