Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Aljazeera cewa, mutanen kasar Jamus kimani dubu 15 ne suka gudanar da zanga zangar yin Allah wadai da yadda gwamnatin kasar take karban baki musamman daga kasashen musulmi.
Wata sabuwar kungiya mai suna “turawa masu kishin kasa da kuma nuna rashin amincewa da musuluntar da kasarsu ta gudanar da zanga zanga ta lumana a gabacin kasar ta Jamus a jiya litinin, wanda ya kafa kungiyar tun watan Octoban da ya gabata ya ce jama’a na tare da su, kuma yawansu na karuwa ta yadda yan siyasar kasar basu isa su yi watsi da su ba.
Ministan sharia na kasar, Heiko Maas, ya ce zanga zangar wani “abin kunya ne ga kasar Jamus wacce ta zama budaddiyar kasa ga baki, kafin haka dai, waziriyar kasar Angela Merkel ta ja kunnen mutanen kasar kan ayyukan kungiyar ta.
Shugaban musulmi na kasar ta Jamus Aiman Mazyek, ya ce akwai tsoron cewa kungiyar, zata raba kan jamusawa tsakanin musulmi baki da kuma yan asalin kasar ta Jamus, kungiyar na mabiya dubu 22 a kasar.
Sai dai mutane dubu 10 ne suka shiga zanga-zagar, banda Amurka kasar Jamus ce kasar da ta fi karban baki daga kasashen duniya musamman daga kasashen musulmi, sannan itace ta fi karfin tattalin arziki a nahiyar Turai.