Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Lagos.Icro cewa, tun daga jiya Litinin ne aka fara gudanar da wani taron baje koli na kur’ani mai tsarki a birnin Lagos babbar cibiyar kasuwancin tarayyar Najeriya da ke samun halartar mutane da dama.
Rahoton y ace wannan baje koli shi ne irinsa na farko da aka fara gudanarwa a tarayyar Najeriya da irin wanann salon na zamani, inda cibiyoyin da ke buga littafan addinin muslunci daga sassa na tarayyar Najeriya suke halartar baje kolin, tare da nuna irin abubuwan da suke bugawa da suka shafi kur’ani mai tsarki.
Daga cikin abubuwan da ake nunawa kuwa har da kwafin kur’ani nauoinsa daban-daban, da wadanda aka buga da inji hakan nan kuma kwai wadanda rubuta da hannu, da kasantuwar Najeriya na daya daga cikin kasashen da musulmin suke yin kokari matuka wajen bayar da muhimmanci ga harkokin kur’ani mai tsarki, kama daga rubutnsa da kuma karatu gami da har.
Haka nan kuma an nuna wasu abubuwa da ake bugawa da suke dauke da ayoyin kur’ani mai tsarki da aka kayata su matuka.
2672225