Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarat cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na SANA cewa, shugaban kasar Syria Bassharul-Assada ya halarci taron maulidin ma'aiki (s.a.wa.) dazu a birnin Damascuss.
Tashar telbijin din gwamnatin Syria ta nuna hotunan shugaba Basshar Asad a daya daga cikin masallatan birnin Damascuss da ake gabatar da bikin maulidin manzon Allah (s.a.wa.) a tare da muffin kasar Ahmad Badruddin Hassun da pira minister Wa'il al-halqy da kuma ministan mai kula da harkokin addini Muhammad Abdul-Sattar al-Sayyid da kuma wasu manyan jami'an gwamnati.
Ministan harkokin addini na kasar ya jaddada kiran da shugaban kasar ya yi a jawabinsa na karshe a farkon wannan watan na janairu da bude tattaunawa a tsakanin dukkanin al'ummar kasar kowace irin akida ta siyasa su ke riko da ita.
A ranar 6 ga watan Janairu da ake ciki ne shugaba Basshar Asad ya gabatar da jawabi a wani dakin taro da ke tsakiyar birnin Damascuss da a ciki ya yi kira bude tattaunawa tsakanin dukkanin bangarorin kasar domin tabbatar da hadin kan Syria.
2672224